Kamata ya yi a ce Nasiru Gawuna da Murtala Garo suna garƙame a gidan yari – Farfesa Hafiz Abubakar
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar ya bayyana cewa kamata ya yi a ce mataimakin gwamnan mai ci Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishinan ƙananan hukumomi, Murtala Sule Garo suna ɗaure a gidan yari a maimakon a ce suna yawonsu a gari da ta kai har an tsayar da su takarar gwamna da mataimaki.
Farfesa Hafiz wanda shi ne ya wakilci mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a gurin taro na musamman akan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano da Cibiyar Bunkasa Demokiradiya ta Mambaya da ke Kano ta shirya, a watan Mayun shekarar 2022.
Tsohon mataimakin gwamnan ya ce al’umma shaida ne akan yadda aka ga fuskokin ƴan siyasar guda biyu a zaɓen gwamna na shekarar 2019, suna ƙoƙarin tayar da tarzoma tare da yunƙurin sace akwatunan zaɓe a yankin ƙaramar hukumar Nasarawa.
Ya ce duniya ta shaida wannan ɗanyen aiki da su ka yi amma abin mamaki shi ne a ƙarshe jam’iyyar APC ta saka musu da tikitin takara a zaɓen shekarar 2023.
Haka kuma Farfesa Hafiz ɗin ya ce Nasiru Gawuna da Murtala Garo sun taka muhimmiyar rawa wajen kai zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2019 matakin Inkwankulusib wanda hakan koma baya ne ga cigaban demokradiyya.
A cikin watan Maris ɗin shekarar 2019 ne jami’an ƴan sanda su kama Nasiru Gawuna mataimakin gwamnan Kano da kuma kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a wancan lokacin bisa zarginsa da yunkurin tafka magudin zaɓe.
© Labarai24
Comments
Post a Comment